Headlines
Loading...
Na Daina Jin DaÉ—in Rayuwa, Burina In Cika Da Imani Kawai, Cewar Alhaji Aminu Dantata

Na Daina Jin DaÉ—in Rayuwa, Burina In Cika Da Imani Kawai, Cewar Alhaji Aminu Dantata

 Na Daina Jin DaÉ—in Rayuwa, Burina In Cika Da Imani Kawai, Cewar Alhaji Aminu Dantata ku kalli vedio 👇👇👇👇



Hamshakin  attajirin nan na Jihar Kano, Aminu Alhassan Dantata, ya ce daina jin dadin rayuwa, kuma ba shi da wani buri sama da cikawa da imani.


Attajirin ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin Mataimakin Dan Takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar APC, Kashim Shettima.


Ya ce ton tasowarsa, ya samu damar haduwa da mutane da dama, kuma ya kulla abota da jama’a a duka jihohin kasar nan.


Sai dai, ya ce a halin yanzu da walan gaske ya samu mutum 10 daga cikin abokan nasa da ke raye.


“Na karade jihohin Nijeriya, kuma na yi harkoki da jama’a a daukacin jihohin, na yi abokai da dama sai dai abin bakin cikin shi ne, da wuya in ambato 10 daga ciki wadanda ke raye.


“Gaskiya a yadda nake yanzu, lokaci kawai nake jira. Ina fata in bar wannan duniya da imani.


“Ina fata ban saba wa kowa ba a rayuwa, idan kuwa hakan ta faru, ina fata za a yi mini ahuwa, ni ma na yafe wa duk wani da ya saba mini.


“A zuri’armu ni kadai na rage, inda nake rayuwa a tsakanin jikoki,” in ji Dantata.


Daga nan, ya yaba da ziyarar da aka kai masa, kana ya yi addu’ar samun dauwamammen zaman lafiya ga Nijeriya da al’ummarta.

0 Comments: