Headlines
Loading...
INNALILLAH WA INNA ILAIHI RAJI'UN👇👇Allah ya karɓi Rayuwar..

INNALILLAH WA INNA ILAIHI RAJI'UN👇👇Allah ya karɓi Rayuwar..


INNALILLAH WA INNA ILAIHI RAJI'UN👇👇👇



Allah ya karɓi Rayuwar Sayyidah A'isha Sheikh Sayyid Ibrahim Sheikh Dahiru Usman Bauchi sanadiyar Haɗarin mota a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja 


Isha ta Kasan ce jika ga Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi kuma jika ga Sheikh Baba Lamin Niasse muna Addu'ar ALLAH ya sada da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam


Muna Miƙa Saƙon Ta'aziyyar mu ga MAULANA Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi da iyalansa da ɗaukacin Ƴan'uwa bisa wannan rashi da muka yi 


ALLAH ya jaddada rahama ga ruhinta Amin.  TARIHIN ABU-HANIFATARIHIN ABU-HANIFA


Abū Ḥanīfa al-Nuʿmān b. Thābit b. Zūṭā b. Marzubān (larabci|أبو حنيفة نعمان بن ثابت بن زوطا بن مرزبان; Ya rayu daga shekara ta c. 699 zuwa shekara 767 CE), An haife shi a shekara ta 699 (80 Hijri)

garin Kufa, Umayyad Caliphate, ya kuma dasu a shekara ta 767 (150 Hijri)


a birnin Baghdad, Dan asalin Parisa ne ( Iran 🇮🇷 ) Shi Dan garin Kufa ne Ya shahara a karantar da fahimtar sa akan Istihsan, ya wallafa shahararren littafin nan wato Al-Fiqh al-Akbar. Malamansa sune; Hammad bin Abi Sulayman, Ata' ibn abi rabah, Zayd ibn Ali, Ja'far al-Sadiq, da sauran manyan tabi'in,


Ya karantar da dalibansa kamar su; Imam Malik Ibn Anas, Imam Al-Shafi'i, Muhammad al-Shaybani, Abu Yusuf, al-Tahawi, Ahmad Sirhindi, Shah Waliullah da sauransu. Anfi saninsa da Abū Ḥanīfa ko kuma Imam Abū Ḥanīfa musamman a wurin mabiya Sunnah, Ya kasance dan karni na 8th ne, mabiyin Sunnah, Malamin Tauhidi kuma Alkali wanda asalinsa bafarise ne. shine yasamar da mazahabar Hanafiyya ko Hanafi Mazhab, wanda har wayau itace Mazhabar dake da mafi yawan mabiya ahlus-sunnah a duniya. Ana kiransa da al-Imām al-aʿẓam ("The Great Imam") and Sirāj al-aʾimma ("The Lamp of the Imams") a wurin mabiya ahlus-sunnah


An Haifi Imamu Abu Hanifa a Cikin Birnin Kufa dake kasar Iraq a lokacin mulkin Kaliphancin Umayyad wato Abd al-Malik ibn Marwan. Mahaifinsa Dan kasuwane daga Kabul dake Afghanistan, mahaifin Imamu Abu Hanifa nada Shekara 40 a duniya aka haifeshi.


Asalin sunan sa An-Nu’uman bin Thabit, At-Taimi, Abu Hanifa Na daga Cikin Manyam Malamai na farko farko da suka yiwa Musulunchi Hikima Bayan Sahabban Manzon ALLAH (💖Sallalahu ALaihi Wa'alihi Wasallam💖), Imamu Abu Hanifa ya rayayi rayuwa da Sahabbain Annabi (💖Sallalahu ALaihi Wa'alihi Wasallam💖), guda 4 daga cikinsu Akwai Anas Bin Malik, Jabir ibn Abd-Allah da kuma Sahl ibn Sa'd (RA).


An haifi Abu Hanifa Shekara 67 bayan Wafatin Annabi (💖Sallalahu Alaihi Wa'alihi Wasallam💖). Kuma Allah ya bashi basira tun yana yaro karami. Har an ruwaito Cewa, Watarana acikin garin Baghdad akwai wani babban kafiri wanda bai yarda da tauheedi ba, kuma bai yarda da cewa akwai Allah ba.

Har ma ya kirkiri wasu tambayoyi yana ta neman wanda zai amsa masa su. Duk Malaman garin sun kyaleshi basu daukeshi da muhimmanci ba.


An haife shi daga cikin Gidan musulunci a garin Kufa, Abu Hanifa yatafi zuwa yankin Hejaz ( yanki Saudi Arabia Ta Yanzu ) dake kasashen larabawa a waccan lokacin yayinda yake matashi, a nan ne yayi karatu a wuraren manyan malaman garin Makkah da Madina. A matsayin sa na Malamin akida kuma mai hukunci, Abu Hanifa yayi suna akan yardarsa da amfani da hankali wurin yin hukunci da ma akida (faqīh dhū raʾy).


A lokacin nan Imam Abu Hanifah ( RA ) yana yaro karami kwata-kwata bai fi shekara goma ba. Watarana yazo wucewa sai yaji mutumin nan yana da Ikirarin cewa wai Musulmai sun kasa amsa tambayoyinsa. Sai Imam Abu Hanifah ya matsa kusa dashi yace masa “In sha Allahu ni zan amsa tambayoyin naka komai wahalarsu”. Mutumin ya amsa gayyatar, Kuma Jama’a suka cika da mamaki. Ta yaya wannan ‘dan Qaramin yaro zai iya jayayya da Kafirin nan wanda manyan Maluma suka kasa ja dashi!


Da ranar Mukabalar tazo sai Jama’ar garin gaba daya suka taru a wani fili a tsakiyar garin Baghdad wanda dama anan ake gabatar da duk wani Muhimmin taro. Sai shi wannan kafirin ya hau kan tudun dake tsakiyar taro. Sannan ya bude muryarsa ya jefo tambayarsa ta farko zuwa ga Abu Hanifah; “Shin menene Allahn naku yake yi dai-dai yanzu? Abu Hanifah ya tsaya yayi tunani na ‘yan mintuna kadan, sai yace ma mutumin “To ina so kai ka sauko kasa, ni kuma in hau sama sannan in baka amsarka”. 


Wannan yaro karamin yaro ‘dan shekara goma (wato Imam Abu Hanifah) ya hau saman kan tudun sannan yace “Ya Allah kaine shaida gareni a gaban duk wadannan Mutanen cewar na shaida lallai yanzun nan kai ka Qaddara saukowar wannan kafiri zuwa Qasa, kuma ka Qaddara cewar Mumini zai hau sama (wato zai daukaka akansa)”.


Da Mutane (‘yan kallo) suka ji wannan amsar ta fito cikin fasaha daga bakin Abu Hanifah, sai suka fara kabbara “Allahu Akbar!” Allahu Akbar!” Tun daga nan kafirin nan ya fara ganin kaskanci.

Amma sai ya sake jefowa tambayarsa ta biyu “Shin meke raye kafin Allahn naku?” (Subhanallah). Imam Abu Hanifah (rah) yayi tunani zuwa wani lokaci sai yace ma kafirin ya Qidaya masa lambobi daga goma zuwa Qasa Sai kafirin ya fara “Goma, tara, takwas, bakwai, shida, biyar, hudu, uku, biyu, daya, sufili Sai Imamu Abu Hanifa yace masa “Shin me ka gani bayan sufili (wato zero)?”


Mutumin yace “Babu komai kafinsa, ni ban sani ba”. Da jin haka sai Imam yayi murmushi yace masa “To gashi nan ka riga ka bawa kanka amsa...Hakika Allah shine rayayye kuma dawwamamme. Babu kowa kuma babu komai kafinsa”. Daga wannan sai waje ya rude da kabbara, suna Qara jinjina ma Imam Abu Hanifah (RA). Kafirin nan zuciyarsa ta harzuka, ransa ya baci. Sai ya jefo tambayarsa ta Qarshe “SHIN YANZU WAJEN INA (WACCE KUSURWA) ALLAHN NAKU YAKE KALLO?” (Shin gabas yake kallo ko yamma ko kudu ko Arewa?). Imam Abu Hanifah bayan yayi tunani zuwa wani lokaci sai yace a kawo masa Fitila (Aci-balbal ko kuma kyandir). Da aka kawo masa sai ya damka wa kafirin nan. Yace masa ya kunna masa, Bayan kafirin ya kunna kyandir din sai ya tambayi Imam Abu Hanifa , to menene dalikin haka? Sai Imam Abu Hanifah yace masa “Shin wanne waje ne wutar hasken kyandir din nan take kallo?” Sai kafirin yace, “Tana kallon dukkan kuskuwoyi ne. (wato gabas, yamma, kudu, arewa, sama da Qasa) Babu inda bata kallo” Sai Imamu Abu Hanifa yace masa “Ai ka riga ka amsa tambayarka. Hakika Hasken Allah ya mamaye ko ina. Yana nan ako ina, babu wajen da babu shi”


Daga nan sai mutane suka rude da kabbarori “Allahu Akbar! Allahu Akbar!! Allahu Akbar!!!”. Shi kansa wannan kafirin yayi mamakin ilimi da basirar Imamu Abu Hanifa (RA). Don haka anan wajen ya furta kalmar Shahada, ya zama Musulmi kuma ya zama Almajirin Imam Abu Hanifah (ra).


Imam Abu Hanifah yana daga cikin mutane mafiya kaifin hankali da basira daga cikin Maluman wannan al'ummar ta Musulunci. Watarana barayi sun shiga gidan wani mutum suka yashe masa dukiyarsa baki 'daya, sannan suka sanyashi ya rantse akan cewa ba zai tona musu asiri ba. Idan kuma ya tona asirinsu to Matarsa ta saku, Saki uku!! Wannan mutum ya wayi gari cikin tsananin bakin ciki. yana kallon mutanen nan suna ta sayar da kayansa da suka sato, amma bashi da damar yace komai, tunda ya riga ya rantse idan ya fallashesu to matarsa ta saku saki uku!! Saboda haka sai yaje ya gaya ma Imam Abu Hanifah halin da yake ciki. Sai yayi Murmushi yace masa "Na san hanyar da zamu bi, kayanka zai dawo ba tare da kace komai ba". Sai Imam Abu Hanifah yasa aka tara masa dukkan Limamai da ladanai na garin, sannan yace musu "Wannan mutumin anyi masa sata ne. amma shin kuna so dukkan kayansa ya dawo gareshi?". Suka ce "Eh". Sai yace to ina so ku tattaro min duk mutanen da aka ta'ba tuhumarsu da sata a unguwanninku.


Da aka tattarosu sai yasa aka kira masa Jami'an tsaro, yace musu ga wasu mutane nan zan rika tambayar wannan mutumin game dasu. Duk wanda kuka ji wannan mutumin yayi shuru bai ce komai akansa ba, to 'barawo ne. ku kamashi. Sai Imam Abu Hanifah yasa aka rika fitowa da mutanen nan 'daya bayan 'daya. Yana tambayar mutumin nan "SHIN WANNAN NE BARAWONKA?". Sai mutumin yace "A'a ba shi bane". Sai ace wannan ya wuce. Amma idan aka tambayeshi "SHIN WANNAN NE BARAWONKA? " in aka ji yayi shuru bai ce komai ba, sai Imam Abu yace "KU KAMA WANNAN SHIMA BARAWO NE".


Da haka sai da aka kama dukkan barayin nan ba tare da mai dukiyar ya ambaci sunayensu ba.

Allah Mai kyauta da karawa kamar Yadda Imamu Abu Hanifa Yake da kaifin basira haka Allah ya Azzurtashi da 'ya mai kaifin Basira. Abu Hanifa ya kasance yana karba tambayoyi tare da bada fatawowi hadi da karantarda dalibban Ilmi.


Wata Rana Sai aka yi masa wata tambaya wacce ta daure masa kai, tambayar kuwa itace; "ME YASA A MUSULUNCE SU MATA BA'A BASU DA DAMAR AUREN MAZA FIYE DA DAYA BA, ALHALI SU MAZA NA AUREN MACCE HAR UKKU?" Wannan tambayar ta daurewa Imam Abu Hanifa kai sosai da Sosai, Cen 'yarsa da ke Zaune Kusansa (wato Hanifa), Sai tace, "Ya Babana ai zan iya karba wannan tambaya Idan har ka amincemin."


Abu Hanifa Ya amince mata akan ta bada amsar wannan tambaya in har ta san amsa. Hanifa ta sa aka tara mata 4 ta bukaci a kawo katon masaki cike da nono, bayan an kawo wannan masaki, Sai tabawa kowace macce kofi daya tace kowacce ta debo wannan Nono dake cikin wannan Masaki. Bayan kowacen su ta debo (Wannan Nonon), Sai tace, dukansu su mayarda nonon a ciki. Dukansu suka sake mayarda nonon da suka diba. Sai Hanifa tace, "To kowaccen ku ta debo Nonon da ta zuba a cikin Wannan masaki, ba tare da ta debo wanda bata zuba ba."


Dukansu sai suka ce, "Taya zamu iya debo nonon da muka zuba kuwa? Alhali nonon ya hade?"

Sai Hanifa Tace, "To kamar hakane, Idan macce ta auri maza biyu ko ukku ko hudu, aka haihu ba za'a iya gano waye mahaifin jarinrin ba." Wannan Amsa ta Sanya Numan bin Thabit (Abu Hanifa) farin Ciki, daga nan sai aka rika kiransa da sunan (Baban Hanifa).


A shekarar 763, Imamu Abu Hanifa ya samu takardar Bukatar yayi Jagorancin alkalin Alkallai daga Al-Mansur a zamanin Kaliph Harun al-Rashid. Lokacin da Wannan takarda ta sami Abu Hanifa sai ya Rubutawa Al-Mansur Cewa, "Hakika ni Ban cancanci Zama kan wannan Mukamin ba abawa wani." Lokacin da Sako ya Zuwarwa Sarki Al-Mansur sai ta yasa aka kira masa Imamu Abu Hanifa Yace Masa Me yasa ba zaka Amsa ba? Abu Hanifa Yace, Ban Cancanta bane kawai.


Al-mansur Ransa ya bace Yace, "Hakika Karya Kake yi domin ka cancanta" Sai Imamu Abu Hanifa Ya buda baki yace, "Babu Shakka bayani na ya tabbata ban cancata Ba, taya zaka dauki Matsayi na Alkalin Alkalai Ka bawa makaryaci?" Wannan amsar ta Abu Hanifa Ita ta harzuka wannan Sarkin nan take ya sa aka kama Imamu Abu Hanifa aka Rufeshi a Gidan kaso (Prison) aka Rika azabantar dashi azaba kala-kala a gidan yarin. 


Duk da Irin Azabar da Imamu Abu Hanifah yake sha masana tarihi sun tabbatarda ci gaba kawai yayi da karantarwa da yin Kira zuwa a kadaita Allah a Cikin Wannan Gidan kaso. A karshe dai wasu malaman tarihi sun bayyana a gidan yarin Allah ya karbi ransa.


Masana tarihi suka ce kusan mutum dubu hamshin (50,000), ne suka halarci zana'izarsa a lokacin da Allah Yayi Masa Cikawa.


Daga cikin littafan da ya wallafa akwai, Fiqh al-Akbar; Fiqh al-Abasat Kitaab-ul-Aathaar, Kitabul Aathaar, Musnad Imaam ul A'zam, da kuma Kitaabul Rad alal Qaadiriyah. Imam Abu Hanifa ya hardace hadisai masu yawan gaske har an ruwaito wani daga cikin magabata na cewa, Imamu Abu Hanifah ba ya rawaito hadisi sai wanda ya haddace, ba ya rawaito hadisin da be haddace ba. Imam Abu Hanifa ya rasu a shekarata (150A.H)


~ B Salia Cisey

0 Comments: