Headlines
Loading...
Yadda Jamila Nagudu Ta Bayyana Cewa Babu Abinda Tafi Bukata Sama Da Aure A Yanzu

Yadda Jamila Nagudu Ta Bayyana Cewa Babu Abinda Tafi Bukata Sama Da Aure A Yanzu

 Yadda Jamila Nagudu Ta Bayyana Cewa Babu Abinda Tafi Bukata Sama Da Aure A Yanzu


👇👇👇

 



Jarumar Masana'antar shirya fina-finai da ke arewacin Najeriya Jamila Nagudu, ta shaida cewa a Yanzu babu abinda tafi muradi sama da Aure.


Jamila Nagudu ta bayyana hakan ne a wata tattaunawa da tayi da sashen Hausa na radio Faransa.


 Ta ce ta shafe sama da shekaru goma tana taka rawar gani a masana'antar, to dole na nemi canji da yafi na irin yanayin da take ciki.


ta ce a baya suna iya fita aiki sama da sau goma ko wanne wata, annan yanzu da harkar ta ja baya bai wuce a wata su fita aiki sau biyu zuwa uku ba.


 Nagudu ta ce duk duniya babu harkar da tafi mata harkar fim, domin juya ita ta iya.


 Kana tana fata idan danta yana da sha'awa ya tsunduma ciki.


Nagudu Ta Bayyana ManyanNagudu Ta Bayyana Manyan Kalubalensu


Da aka tambayeta ko wanne kalubale suke fuskanta? Nagudu ta ce kalubalen bai wuce yadda suke fuskantar barazana daga masu fassara fina-finan India zuwa Hausa ba, domin a cewarta hakan ya sanya sun samu koma baya sosai.


ga cikakkiyar tattaunawar"Muna siyar da Film kaset daya a Naira 300, da fassarar fim din India yazo sai ta ke Siyar da guda biyar a Naira 100.


 Hakan yasa dole sai mutun ya sai na Naira 100 yaje yayi sati yana kalla a gidansa madadin ya sai guda daya Naira 300" inji Nagudu.


A karshe Nagudu ta shawarci abokan sana'arta kan su kara jajircewa, domin zama jarumi ko jaruma ba karamin abu bane, yana matukar bukatar sadaukarwa da bada lokaci da kuma biyayya.

0 Comments: