Headlines
Loading...
Mutane 5 Da Likitoci Suka Mokaɗarwa Da Fuskoki Yayin Ƙoƙarin A Canza Kamanninsu

Mutane 5 Da Likitoci Suka Mokaɗarwa Da Fuskoki Yayin Ƙoƙarin A Canza Kamanninsu

 

Mutane 5 Da Likitoci Suka Mokaɗarwa Da Fuskoki Yayin Ƙoƙarin A Canza Kamanninsu

Dana nan👇👇



Yayin da wasu ke kashe maƙudan kuɗaɗe wurin ganin sun sauya halittarsu, wasu kuma sun yi ƙoƙarin ganin sai sun yi kama da wasu fitattun jarumai. Ga mutane 5 da aikin likitoci suka yi gardama a kan su, Buzzloaded.com ta ruwaito:

Mutane 5 Da Likitoci Suka Mokaɗarwa Da Fuskoki Yayin Ƙoƙarin A Canza Kamanninsu

Jordan James Parkes:

Wani matashi ne dan kasar Amurka da ke kwalliya kuma yana matukar burin kama da Kim Kardashian. Za ka sha mamaki kan ganin yadda ya yi fiye da ayyuka 50 inda ya kashe sama da dala 150,000. Sai dai ko da ya kashe kudaden bai yi kama da ita ba, sai aka lalata masa halittarsa.

Sarah:

Matashiyar ‘yar kasar Iran ce kuma ta yi iyakar kokarinta wurin ganin likitoci sun mayar da ita mai kama da Angelina Jolie. Saidai abin ya ci tura inda suka mayar da iya tamkar gawa. Ta yi fice a kafafen sada zumuntar zamani ne bayan ta wallafa hotunanta a shekarar 2017 inda jama’a suka dinga zundenta.

PixeeFox:

Yayin da saura ke kokarin kama da ‘yan uwansu bil’Adama, ita burin Pixee shi ne kama da ‘yan aljanu. Ta ya iyakar kokarinta inda sai da ta sanya aka cire mata kasusuwan kirjinta guda shida sannan ta mayar da kwankwasonta inci 14. An yi mata ayyuka fiye da 200 duk don ganin ta sauya halittarta.

Herbert Chavez:

Ya shiga littafin tarihi na Guiness, kasancewar ya yi kokarin komawa tamkar super man. Ba abin mamaki bane tunda ya ce tun yana karamin yaro mai shekaru 4 yake matukar kaunar Superman. An yi masa ayyuka 13 don ganin halittarsa ta koma irin ta Superman.

Oli London:

Yana daya daga cikin mutanen rukunin pop da ke duniya. Yana matukar kama da Park Jimin ne. Kuma ya yi fice ne a shekarar 2018 bayan sun a bayyana a wani shirin turawa mai suna “Hook on the look”. Oli ya kashe fiye da dala 200,000 wurin yin ayyuka.

Yadda Likitoci A Amurka Suka Yi Tururuwa Don Kula Da Jinjirin Birin Da Ya Kamu Da Ciwon Sanyi

Masha Allah Kalli Yadda Ummi Rahab Take Yiwa Mijinta Addu’a A Saudiyya

Likitocin Sun Cika Wadonsu Da Iska Bayan Zaki Ya Farka Jim Kaɗan Bayan Masa Allurar Bacci

Yadda Tsohon Mijin Momee Gombe Ya Durawa Wani Ashar Bayan Da Yace Ya Yi Sakin Wawa

0 Comments: