Headlines
Loading...
Shekara 7 na yi ina rubuta waƙar da nai wa Manzon Allah — Alan Waƙa

Shekara 7 na yi ina rubuta waƙar da nai wa Manzon Allah — Alan Waƙa

Shekara 7 na yi ina rubuta waƙar da nai wa Manzon Allah — Alan Waƙa

Dana nan 👇👇

 Shaharran mawakinnan Hausar nan, Aminuddeen Ladan Abubakar', wanda aka fi sani da Alan Waka, ya ce ya dauki kimanin shekaru 7 ya na rubuta wakar da ya yiwa fiyayyen halitta, Manzon Allah (S.AW), wacce ya sanyawa suna "Muhammadu miftahul futuhati linzamin rayuwata".


Yace ya kwashe shekarun ne kafın ya kammala rubuta wakar saboda sai da ya gudanar da bincike mai zurfi, inda ya kara da cewa wakar ta shafi tarihin rayuwar Annabi Muhammad (SA W) tun daga haihuwa har zuwa wafatin sa.


"Irin wannan babban aiki yana matukar bukatar bincike na tarihi da kuma irin kalmomin da za'a yi su akan Fiyayyen Halitta, don gudun zarmewa". Inji Alan waka


Hakazalika yace ita waka "Mufitahul futuhati" littafi ne ya mayar da shi waka saboda mutane da dama su amfana, inda ya kara da cewa babu shakka mutane sun ji dadin wakar "kuma nima Ina alfahari da ita."


Ya ce mafiyawan wakokinsa yana gina sune kan llimi kuma yana gudanar da bincike kafın yayi kowacce irin waka, inda ya ce "domin yin hakan shi yake bani damar fadin abun da yake dai-dai akan duk wanda zai yiwa waka."

0 Comments: