Headlines
Loading...
An Guntule Kan Shugaban Karamar Hukuma Bayan Karbar Diyyar N6m

An Guntule Kan Shugaban Karamar Hukuma Bayan Karbar Diyyar N6m

 

An Guntule Kan Shugaban Karamar Hukuma Bayan Karbar Diyyar N6m

Dan nan 👇👇👇



An dai sace Chris ne tare da wasu mutum biyu ranar Juma’a a kauyensu da ke Imoko a yankin Arondizuogu. Maharan sun kuma farmaki ilahirin kauyen nasa.

An ce maharan dai sai da suka harbi mutumin a ka kafin su yi awon gaba da shi.

Wakilinmu ya ga wani bidiyon Kantoman yana durkushe da gwiwoyinsa a kasa, yayin da masu garkuwar da shi suke gargadin Gwamnan Jihar, Hope Uzodinma cewa shi ma hakan za ta faru da shi nan ba da jimawa ba.


Alfijr ta rawaito Kasa da awa 48 bayan an sace Kantoman Karamar Hukumar Ideato ta Arewa da ke jihar Imo, Chris Ohiu, an tsinci gawarsa ba kai.

An guntule kan nasa ne ranar Lahadi, bayan wasu ’yan bindiga sun sace shi.

Bayanai sun nuna cewa an sare kan nasa ne bayan an karbi kudin fansar Naira miliyan shida.


0 Comments: