Headlines
Loading...
Darasi Daga Rayuwar Matuƙiyar Jirgin Sama Wacce Ba Ta  Da Hannu

Darasi Daga Rayuwar Matuƙiyar Jirgin Sama Wacce Ba Ta Da Hannu

 Darasi Daga Rayuwar MatuÆ™iyar Jirgin Sama Wacce Ba Ta Da Hannu 👇👇




Matashiya Jessica Cox mai shekaru 39 ƴar ƙasar Amurka, wacce ta girma ba tare da hannaye a tare da ita ba, ita ma ta tabbatarwa da duniya cewa tabbas babu wani nakasasshe sai kasasshe, ta hanyar jajircewa da kuma nuna ƙwazo wajen neman ilimi har ta cimma muradin ta, da kuma kafa tarihi a duniya, na zama nakasasshiyar matuƙiyar jirgin sama (pilot) wacce aka ba lasisin tuƙi ta farko a duniya.


Darasi Daga Rayuwar Matuƙiyar Jirgin Sama Wacce Ba Ta Da Hannaye!

Rashin hannu bai sanya zuciyar Jessica ta mutu ba, har tayi tunanin cewa kamar ba zata iya yin komai ba, ko kuma ba zata iya amfanawa duniya komai ba. 

A yanzu haka wannan baiwar Allah tana É—aya daga cikin manyan Æ™wararrun matuÆ™a jirgin sama a wani kamfani a Æ™asar Amurka, tana kuma samun albashi da tagomashi mai tsoka, tana kuma gudanar da rayuwar ta cikin farin ciki tare da iyalanta da sauran Æ´an’uwanta.


A shekarar 2015 ta samu nasarar wallafa wani littafi da ta rubuta mai suna (Disarm Your Limits: The Flight Formula to Lift You to Success and Propel You to the Next Horizon). 

Wannan littafi ya karɓu sosai, saboda muhimman saƙonni na ƙarfafa gwiwa da ke tat


tare da wannan littafi.

Tabbas akwai darasi mai yawa a tattare da wannan É—an takaitaccen labari na Jessica Cox. HaÆ™iÆ™a babu nakasasshe sai wanda ya bari zuciyar sa ta nakasa, har yake tunanin cewa nakasa za ta iya hana shi yin wani da zai amfani kanshi da ma sauran al’umma.

Allah (S.W.T) Ka ci gaba da yi mana katangar ƙarfe da nakasar zuciya, Ka ci gaba da ba mu ikon fahimtar abun da shi ne daidai, Amin

0 Comments: